News
DA ƊUMI-ƊUMI: Makiyaya Sun Kashe Mutane Biyar Bayan

Daga Muhammad zahraddin
Al’ummar Arimogija da ke karamar hukumar Ose a jihar Ondo ta shiga rudani a yammacin ranar Litinin din da ta gabata yayin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kai wani sabon hari a garin, inda suka kashe mutane biyar.
Harin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki garin Omolege da ke kan iyaka a karamar hukumar, inda suka kashe mutane uku tare da kona gidaje da dama.
An ce shugaban al’ummar na cikin wadanda aka kashe.
A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Rotimi Akeredolu ya ziyarci yankin karamar hukumar inda ya sha alwashin farautar wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Gwamnan ya ziyarci wurin ne tare da kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Oyediran Oyeyemi; Kwamandan Rundunar Amotekun, Tunji Adeleye; da wasu ‘yan majalisar zartarwa ta jiha.
Sai dai kuma, sa’o’i kadan bayan ziyarar, SaharaReporters ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai hari a wata al’umma a karamar hukumar, inda suka kashe akalla mutane biyar.
Wadanda aka kashe sun hada da shugaban matasan yankin, Augustine Lucky; Osaromere Augustine; Odalume Stephen; Okpakoro da Monday Black.