News
Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya na riƙon ƙwarya, Shonekan ya rasu
Daga kabiru basiru fulatan
Chief Ernest Shonekan, Jagoran Gwamnatin Riƙon Ƙwarya wacce ta gaji mulkin soji na Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya rasu.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa Shonekan ya rasu a wani asibiti a Jihar Legas yana da shekara 85 da haihuwa.
A tuna cewa marigayin shine Shugaban Gwamnatin Riƙon Ƙwarya da ga 26 ga Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamba a shekarar 1993 kafin Marigayi Janar Sani Abacha ya karɓe mulkin ƙasar zuwa 1998.
Ƙarin bayani na nan tafe…