Connect with us

News

Shirin ciyar da ɗalibai na bana zai magance yunwa tsakanin yara — Minista

Published

on

Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Gwamnatin Taraiya ta baiyana cewa shirin ta na ciyar da ɗalibai,ai ƙara samun haɓɓaka ta musamman.

Sadiya Farouq, Ministar Jin-ƙai, Kula da Ibtila’i da Tallafawa Al’umma ce ta baiyana haka a wata sanarwa da Halima Oyelade, Jami’arta ta musamman kan Harkokin Sadarwa ta zantawa hannu a Abuja a yau Laraba.

Ta ce Ma’aikatar ta, da haɗin gwiwar tsarin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, za ta bunƙasa shirin domin ya magance yunwa a tsakanin yara.

Advertisement

Tace bunƙasar shirin zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da ƙara yawan yaran da a ke sa yawa makarantun da kuma rage fashi a makarantun firamare.

“Wannan sakamakon wani nazari da a ka yi ne a wata ukun farko na 2021 na gano hanyoyin da za a riƙa bunƙasa Slshirin ciyawar da kuma ɗorewa wajen aiwatar da shi.

“Hakan kuma ya nuna a kwai nasarori. Sai dai za mu ƙara dagewa mu ƙara bunƙasa shirin.

Advertisement

“Tsarin ya na ƙara wayar da kai wajen samun abinci mai gina jiki, halaiyar cin abinci, samar da ilimi. Sannan ya na bunƙasa faɗaɗa noman abinci musamman abincikan mu na gargajiya,” in ji ta.

Ministar ta ƙara da cewa shirin ciyar da ɗaliban na ɗaya da ga cikin shirye-shirye na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ya fi ji da su.

 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *