News
YANZU- YANZU Matuka baburan a daidaita sahu suka janye yajin aiki
Daga kabiru basiru fulatan
Gamayyar kungiyar matuka baburan adaidaita sahu sun janye yajin aikin da suka kwashe kwanaki uku suna yi.
Lauyan yan kungiyar Barrister Abba Hikima ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema labarai a daren yau Laraba.
Sai dai bai yi cikekken bayani ba game da matsalar da aka cimma tsakaninsu da gwamnatin jihar Kano ba.