News
Ranar Tunawa da Ƴan Mazan Jiya: Gwamnatin Taraiya ta bada umarnin rufe titunan da ke yankin Sakateriyar Taraiya
Daga Yasir sani Abdullah
A yau Juma’a ne Gwamnatin Taraiya ta bada umarnin rufe duk titunan da ke yankin Sakateriyar Taraiya da na Maikatar Harakokin Waje a Abuja.
Shugabar Ma’aikata na Taraiya, Dakta Folasade Yemi-Esan ce ta bada umarnin a yau a wata sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar, Abdulganiyu Aminu ya fitar.
A cewar Yemi-Esan, rufewar ta biyo bayan bikin tunawa da ƴan Mazan jiya na 2022.
Sanarwar ta ce a bikin, wanda z a yi a gobe Asabar, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da sauran jami’an gwamnati za su je a gurin bikin domin karrama ƴan Mazan Jiya da su ka rasa rayukansu a wajen yaƙi.
Jaridar indaranka ta rawiato cewa a kowacce ranar 15 ga watan Janairu, rana ce ta bikin tunawa da sojojin Nijeriya da su ka rasu a wajen yaƙi da wasu ƙasashen.
-
News5 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News7 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
