News
Zargin ƙazafi: Gwamna Masari ya nemi ƴan jaridar Abuja su biya shi diyyar N10bn

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya bukaci Ƙungiyar ƴan Jarida ta Ƙasa, NUJ, reshen Abuja da ta biya shi diyyar Naira biliyan 10 biyo bayan wata sanarwar manema labarai da su ka fitar, inda ya ke zargin sun ɓata masa suna.
Masari ya kuma buƙaci ‘yan jaridun da su bayar da haƙuri a hukumance a jaridun ƙasa guda takwas nan da kwanaki bakwai masu zuwa ko kuma su fuskanci hukuncin Shari’a.
Da yake zantawa da manema labarai a Katsina, a ranar Alhamis, Lauyan Masari, E.O. Obunadike, ya ce wanda ya ke karewa ya yanke shawarar daukar irin wannan matakin ne domin kare mutuncinsa da ya gina shi ashekaru da dama.
Idan dai ba a manta ba, ‘yan jaridan biyu Emmanuel Ogbeche da Ochaika Ugwu, shugaba da sakataren NUJ ne su ka fitar da wata sanarwa a ranar 2 ga watan Janairu, inda su ke zargin Masari ya bayar da umarnin kama Nelson Omonu na jaridar Summit Post a Abuja.
Sun yi zargin cewa gwamnan ya bayar da umarnin kama Nelson a Katsina bayan ya zarge su da ɓata masa suna.
Sai dai kuma da ga bisani Ugwu da Ogbeche sun fitar da wata sanarwa inda suka nemi gafarar Gwamna Masari, saboda sun zaci ya bada umarnin kama shi.
Amma Obunadike, ya ce haƙurin nasu bai isa ba, don haka ya ce ‘yan jaridar su bada hakurin a jaridu takwas na kasa, baya ga biyan diyyar Naira biliyan 10.