Connect with us

News

2023: Atiku zai yi zangon mulki ɗaya ne kawai ya miƙawa Igbo – Dokpesi

Published

on

FB IMG 16431165098711370
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

Shugaban kwamitin ƙwararru na yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, Raymond Dokpesi, ya nemi goyon bayan a bar Atiku Abubakar ya yi zangon mulki ɗaya a zaɓen 2023.

Ya ce idan aka zaɓi Abubakar na tsawon zangon mulki guda na shekaru huɗu, hakan zai ba da dama ga yankin Kudu-maso-Gabas, yankin da ‘yan kabilar Igbo suka mamaye, su samar da shugaban ƙasa a 2027.

A cewar wani rahoto da jaridar The Punch ta wallafa, Dokpesi, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin yayin da ya ke magana a Umuahia, babban birnin jihar Abia.

Advertisement

Ya ci gaba da cewa, Abubakar, wanda ya fito daga shiyyar siyasar Arewa-maso-Gabas, shi ne mutumin da ya dace ya karɓi mulki daga hannun Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Dokpesi ya je sakatariyar jam’iyyar PDP ta jihar domin tattaunawa da shugabannin jam’iyyar a jihar.

Dokpesi ya baiyana cewa ba yi amfani da tsarin shiyya na PDP a lokacin zaɓen shugaban kasa na 2015 ba, sakamakon haka jam’iyyar ta shiga zaben da rarrabuwar kai wanda a ƙarshe ta sha kaye.

Advertisement

Ya kara da cewa dole ne jam’iyyar PDP ta sake baiwa Arewa damar cika shekaru huɗu da ta yi tana shugabancin kasar domin ta kwace mulki daga hannun APC a 2023.

Ya kuma ba da tabbacin cewa jam’iyyar PDP za ta miƙa mulki zuwa shiyyar Kudu maso Gabas da kuma tabbatar da cewa shiyyar ta samar da shugaban kasa a 2027.

Ya ce, “Jam’iyyarmu ta yi imani da cewa za a yi wa ofishin shugaban kasa mulki a tsakanin Arewa da Kudu har tsawon wa’adi biyu na shekaru takwas.

Advertisement

“Don haka ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya mika wa Marigayi Umaru Ya’Adua, amma bayan rasuwarsa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karbi mulki ya kamala wa’adinsa na farko.

“Jonathan, ya kuma nemi karin shekaru hudu da aka ba shi, amma da ya fara neman wani wa’adi a 2015, Arewa ta ga ya saba wa yarjejeniyar shiyyar da jam’iyyar ta yi.

“Saboda haka muka shiga zaben da rabe-raben majalisa muka sha kashi. Shi ya sa muka yi nuni da cewa mu yi kokawa da mulki daga APC muna bukatar dan takarar shugaban kasa mai karfi daga Arewa.

Advertisement

“Tunda an yi imanin cewa Arewa-maso-Gabas da Kudu-maso-Gabas su ne yankuna biyu na siyasa da ba su samar da shugaban kasa ba. Mun ji cewa Atiku, wanda ya fito daga Arewa maso Gabas, shi ne dan takara mai karfi a wannan aiki.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *