News
Nan Da Shekarar 2023 Ƴaƴana Za su Kai 30,Har Yanzu da Karfina -Alhassan Ado Doguwa

Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa ya sanya zauren majalisar dariya yayin da ya bayyana cewa ya da burin hada ‘ya’ya 30 cif kafin 2023.
Alhassan Ado, mai shekaru 56, wanda ke wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada a majalisar wakilan Najeriya shi ne dan majalisar da yafi jimawa a majalisar.
Doguwa ya zama dan majalisa a shekarar 1992, bayan kammala karatun jarida a jami’ar Bayero ta Kano.
An sake zabensa a shekarar 2007 inda yake rike da mukamin har yanzu.
A zaman majalisar na jiya, Alhassan Ado ya sanar da cewa daya daga cikin matasan 4 ta haifi diya mace.
A yanzu dai dan majalisar yana da ‘ya’ya 28, inda ya ce akwai wasu nan gaba.
Ya yin da yake mayar da martani ga jawabin taya murna da shugaban marasa rinjaye na majalisar, Ndudi Elumelu, Doguwa ya ce har yanzu fa da kwarinsa.
Ya bayyana cewa jaririyar da mahaifiyarta suna nan kalau.
Alhassan Ado ya kara da cewa, muradinsa shine ya cika ‘ya’ya 30 kafin 2023.