News
Ƴan Sanda sun cafke babban ɗan adawar Ganduje, Muaz Magaji ‘Yan
Daga Yasir sani Abdullah
‘Yan Sanda sun kama Muaz Magaji, ɗaya daga cikin masu sukar gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje.
Ƴan sanda sun kama shi ne bayan wata hira da aka yi da shi kai tsaye a gidan talabijin na Trust TV da ke Utako, Abuja da misalin karfe 9:15 na dare.
Ko da yake har yanzu ƴan sanda ba su ce uffan ba kan kamun nasa, shaidun gani da ido sun shaida wa jaridar DAILY NIGERIAN cewa jami’an ƴan sanda sun biyo Magaji a baya bayan ya bar ofishin gidan talabijin ɗin.
“Bayan ‘yan mintoci da suka gabata wani abin takaici, damuwa da nadama ya faru a hanyar Ngozi Okonjo Iwela ta hanyar TOS Benson Crescent junction. Injiniya Magaji Muazu ya yi hatsari ne inda a ka hankaɗa motarsa kirar Honda ta sauka daga kan titin sannan ta daki wata sandar fitilar titi. Duk da cewa ya fito daga cikin motar bai ji rauni ba, amma duk jakunkunan Airbags sun fito waje.
“Da alama aikin ‘yan sanda ne domin nan take su ka kama shi su ka kai shi caji-ofis na Utako da ƙarfin tsiya. Yayin da nake rubuta wannan bayani na kasance a wurin ina tsare motarsa kuma yanzu muna kan hanyarmu ta zuwa ofishin ‘yan sanda. Jakarsa da batirin motarsa suna tare da ni,” inji wani ganau.
A tuna cewa a ranar 17 ga watan Janairu, ‘yan sanda a Kano sun gayyaci Magaji domin ya amsa tambayoyi dangane da karar da aka shigar a kan sa.
Sai ya aika lauyoyinsa zuwa ga rundunar maimakon ya bayyana a gabansu da kan sa, sannan ya shigar da kara na tabbatar da tsaro a kan ‘yan sanda.
Ganduje ya kori Magaji, wanda tsohon kwamishinan ayyuka da aiyukan more rayuqa saboda “kalaman rashin ɗa’a” da ya yi kan rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.
Tun bayan barin gwamnati, tsohon kwamishinan ya rika sukar gwamnan kan salon shugabancinsa da kuma shigar da iyalansa cikin harkokin mulki a jihar.
Biyo bayan fitowar bangaren jam’iyyar APC a jihar na Sanata Shekarau, sai tsohon kwamishinan ya koma bangaren.