Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo: Liverool da City na son Bukayo Saka, United za ta yi garambawul, makomar Rudiger

Published

on

123143324 60c08aaf 5644 4943 835d e63e2d0f4a18.jpg
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

Manchester City na sha’awar sayen dan wasan bayan Uruguay Ronald Araujo, mai shekara 22, wanda ya dakatar da tattaunawa da Barcelona. (Sport – in Spanish)

Har ila yau Manchester United na shirin yin tayin sayen Araujo, wanda yarjejeniyarsa ta Barcelona za ta kare a shekarar 2023. (Marca – in Spanish).

United ta shirya tsaf domin fafatawa da Bayern Munich da Barcelona a yunkurin dauko dan wasan baya na Netherlands Matthijs de Ligt mai shekara 22 daga Juventus. (Calciomercato – in Italian)

Advertisement

Har wayau United din na shirin yin garambawul a tsakiyarta a bazara, inda za ta dauko dan wasan West Ham Declan Rice, mai shekara 23, da abokin wasansa na Ingila Kalvin Phillips mai shekara 26 daga Leeds da kuma dan kasar Mali na RB Leipzig Amadou Haidara, mai shekara 24 (ESPN)

Chelsea ta kasa yin wani sabon yunkurin kulla yarjejeniya da dan wasan baya na Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 28 (Mail)

Shugaban kulob din Adana Demirspor Murat Sancak ya ce kulob din ya amince da daukar Dele Alli a matsayin aro daga Tottenham kafin dan kasar Ingilan mai shekaru 25 ya koma Everton kan yarjejeniyar shekara biyu da rabi. (Milliyet – in English).

Advertisement

Liverpool da Manchester City za su iya zawarcin dan wasan Ingila Bukayo Saka mai shekaru 20 idan Arsenal ta kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai ta badi. (ESPN)

Atletico Madrid ta ci gaba da nuna sha’awar daukar dan wasan bayan Aston Villa na Poland Matty Cash, mai shekara 24, gabanin kakar wasa mai zuwa. (Fabrizio Roma

Chicago Fire na dab da daukar dan wasan tsakiyar Switzerland Xherdan Shaqiri, mai shekara 30, daga Lyon. (MLS Foot Ball)

Advertisement

Dan wasan gaba na Palmeiras, mai shekara 15, Endrick, wanda tuni aka alakanta shi da Barca da Real Madrid, ya ce dukkan matasan ‘yan wasan Brazil na son bugawa Barcelona wasa. (Sports Daily)

Watford ta gaza wajen siyan dan wasan bayan Manchester United Phil Jones, mai shekara 29, kafin rufe kasuwar musayar ‘yan wasa ta Janairu. (Insider Football)

Manchester City ta bi sahun West Ham da Brentford wajen nuna sha’awar dan wasan Sheffield Wednesday mai shekara 16 Bailey Cadmarteri. (Sheffield Star)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *