News
Luguden wuta ta jiragen yaƙi ya sanya ƴan ISWAP 25 sun lume a kogin Marte
Daga yasir sani abdullahi
Yayin tserewa luguden wuta ta jiragen yaƙi na sojojin Nijeriya, ƴan ƙungiyar ƴan ta’adda ta ISWAP sun 25 ne su ka lume a wani kogi mai zurfi a ya kin Marte da ke ɓangaren Tafkin Chadi a Arewa-maso-Gabas.
Tun ranakun Laraba da Alhamis jiragen yaƙin sojojin, da su ka haɗa da ‘Super Tucano’ na Rundunar Sojin Sama ta Ƙasa, NAF su ka yi luguden wuta kan sansanonin ƴan ta’addan a wasu hare-hare da su ke yi na tsawon mako ɗaya.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa jaridar PRNigeria cewa jiragen yaƙin sun saki bama-bamai a sansanoni da wajen ajiye kayaiyakin ƴan ta’addan.
Majiyar ta ce an kakkai hara-haren ta jiragen yaƙin sojoji ne a Bukar Mairam Jubularam, Abbaganaram da Chikul Gudu duk a lokaci ɗaya, inda aka tashi guraren ajiye kayaiyakin su sannan a ka kashe ƴan ISWAP ɗin da dama.
A cewar majiyar, yan ISWAP ɗin da su ka tserewa luguden wutar a Bukar Mairam da Jubularam, sun yi ƙoƙarin su tsallake kogin amma wajen 25 da ga cikin su su ka nutse kuma su ka rasa rayukansu.
Majiyar ta ƙara da cewar hare-haren sam da a ke kaiwa ƴan ISWAP a-kai-a-kai ne ya sanya a ka tarwatsa shirye-shiryen su na kai hare-hare kan rundunonin sojoji.