News
Sule Lamido: Ba na goyon bayan mulkin karba-karba
Tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya Alhaji Sule Lamido ya ce ba ya goyon bayan mulkin karba-karba.
Ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa.
“Idan an zo batun karba-karba zan ce ni ban yarda ba. Kamata ya yi a kalli duniya yadda take, koina an ci gaba; ko ina ana maganar gina dan adam. Don haka ya kamata a ga cewa me za mu yi domin ci gaban Najeriya a matsayinmu na jagorar bakaken fata,” in ji shi.
Ya kara da cewa a halin da ake ciki babban abin dubawa wajen zaben shugaba shi ne nagarta ba addini ko kabila ko kuma sashen da mutum ya fito ba.
Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya kuma yi wa Shugaba Muhammadu Buhari shagube game da cire tallafin man fetur, yana mai cewa a baya Buhari ya rika karyata jam’iyyar PDP game da tallafin mai amma yanzu shi da kansa ne yake batun tallafin na mai.