Connect with us

News

Kasuwar musayar ƴan ƙwallo: Barca na daf da kammala cinikin Azpilicueta, makomar Rudiger da Isak

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

Barcelona na fatan kammala cinikin dan wasan bayan Chelsea na Spain Cesar Azpilicueta, mai shekara 32, da dan wasan bayan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 25, cikin ‘yan kwanaki. (Express)

Manchester United ta bi sahun Arsenal wajen zawarcin dan wasan gaban Real Sociedad Alexander Isak mai shekaru 22, inda kulob din na Old Trafford ke kallon dan wasan gaban Sweden a matsayin wanda zai maye gurbin Cristiano Ronaldo. (Football in London)

Advertisement

Haka kuma United ɗin da Chelsea za su fafata a kan ɗan wasan tsakiya na Ingila Declan Rice, mai shekara 23 a bazara. (Sky Sports)

Shugaban Lille, Olivier Letang, ya ce dan wasan baya na Netherlands Sven Botman, mai shekara 22 wanda aka alakanta shi da komawa Newcastle a watan Janairu ya cancanci taka leda a kungiyar da za ta iya lashe gasar zakarun Turai. (Le Parisien)

Wakilan tsohon dan wasan West Ham da Manchester United da Manchester City Carlos Tevez na tattaunawa da kungiyar DC United ta MLS. Dan kasar Argentina, mai shekaru 38, ya riƙa yawo a kyauta tun bayan barin Boca Juniors a watan Yulin bara. (The Athletic)

Advertisement

Manchester United ta amince da biyan fan miliyan 12 ga Flamengo kan Andreas Pereira, kulob din da ke kasarsa inda dan kasar Brazil din mai shekara 26 ke zaman aro. (Mirror)

Tsohon dan wasan Ingila Kevin Phillips ya ce Liverpool za ta iya siyan Bukayo Saka na Arsenal don maye gurbin Mohamed Salah na Masar(Football Insider)

Dan wasan baya na Chelsea da Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 28, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana, yana son fan 225,000 a duk mako domin ya ci gaba da zama a Stamford Bridge, inda Blues din za ta rika bayar shi fam 140,000 duk mako. (Mirror)

Advertisement

Daraktan RB Leipzig, Oliver Mintzlaff ya hakikance cewa dan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 24, Christopher Nkunku zai ci gaba da zama a kungiyar duk da sha’awar Liverpool da Arsenal suka nuna ta ɗaukarsa. (Sky 90)

Paris St-Germain ta taya dan wasan bayan Faransa Layvin Kurzawa, mai shekara 29 (Le Parisien)

Dan wasan tsakiya na Barcelona Gavi, mai shekara 17, ya ki amincewa da tsawaita kwantiragi saboda albashin da ake ba shi a ƙungiyar bai masa ba (Sports In Spain).

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *