News
Majalisar Zamfara ta miƙawa Mataimakin Gwamna sanarwar tsigewa
Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Majalisar dokokin Jihar Zamfara ta ce ta miƙa wa Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu takardar sanarwar tsige shi da ga muƙamin sa.
Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Hon. Shamsudeen Bosko ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai matsayin majalisar jihar kan shirin tsige mataimakin gwamnan a jiya Litinin.
Ya sha alwashin cewa babu abin da zai hana ƴan majalisar dokokin jihar tsige mataimakin gwamna saboda an same shi da laifuka guda uku da a ke zarginsa kuma in sun tsige shi za su maye gurbinsa da wani mai kishin jihar.
Zarge-zargen da a ke tuhumar Aliyu da su sun haɗa da karya kundin tsarin mulki, karya ka’idar ofishinsa da kuma almundahanar kuɗaɗe.
‘Yan majalisar sun yi ikirarin cewa Mataimakin Gwamnan ya saɓa wa sashe na 190 da 193 (1) (2) A, B da C na kundin tsarin mulkin Taraiyar Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka yi masa kwaskwarima).
Bosko ya kuma jaddada cewa majalisar dokokin jihar ta cika sharuɗɗan sashe na 188 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda kashi daya zuwa biyu bisa uku na ‘yan majalisar gaba daya sun amince da tsige Mataimakin Gwamnan.
Sai dai babban sakataren mataimakin gwamnan, Umar Gusau a lokacin da Gidan Talabijin na AIT ya tambaye shi kan ko shugaban nasa ya samu sanarwar tsige shi daga majalisar dokokin jihar, ya ce ofishin mataimakin gwamnan bai samu wani sako daga majalisar ba.
Ya kuwa Kara da cewa mataimakin gwamnan ta hannun lauyansa ya aike wa majalisar dokokin jihar Umarnin kotu Wanda ya hana ‘yan majalisar ci gaba da shirin tsige Mataimakin Gwamnan Jihar ta Zamfara.
Tun a 2021ne dai rikici ya ɓarke tsakanin Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle da Aliyu sakamakon ƙin bin gwamnan zuwa Jam’iyar APC da ga PDP.