Hukumar kula da lamurran ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta sake jaddada kira ga ‘yan ƙasar mazauna Ukraine da su “ankare” kuma su “rage tafiye-tafiye” musamman zuwa gabashin ƙasar.
Kiran na zuwa ne yayin da ake ta nuna fargaba kan yunƙurin Rasha na afka wa maƙociyarta Ukraine, inda ta jibge dakaru 100,000 a kan iyaka.
Tun a ƙarshen watan Janairu ne Nigerians in Diaspora Commission ta gargaɗi ‘yan Najeriya da su kula da tsaron lafiyarsu sannan ta ba su shawara kan yadda za su tuntuɓi ofishin jakadancin ƙasar a Ukraine.
Rasha ta sha musanta batun cewa tana shirin mamaye maƙociyar tata.
Tuni Amurka ta umarci ‘yan ƙasarta da su fice daga Ukraine ɗin.