Sports
Yan wasa biyar da suka juya wa Ingila baya saboda Nijeriya
Daga
muhammad muhammad zahraddin
A lokuta da dama, yan wasan nahiyar Afrika da aka haifa a Turai ko kuma suka tashi a can sukan sauya sheka daga ainihin kasarsu zuwa wadda suke rayuwa a cikin.
An samu manyan ‘yan kwallon Afrika da suka wayi gari suna bugawa kasashen Turai kwallo, bayan an yi musu rijistar zama ‘yan kasa.
Sai dai cikin yanayin ban mamaki labarin ya sauya kan wasu ‘yan kwallo da ba a taba zaton hakan zai faru ba a kansu, wadanda suka juya wa Ingila Baya suka sanya wa Najeriya riga.
Fifa ta yarda Lookman ya koma Nijeriya
Dan wasan gefe na Leicester City Ademola Lookman yanzu zai iya wakiltar Nijeriya a mataki na Super Eagles bayan hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta amince da bukatarsa ta neman buga gasar cin kofin Afrika karo na uku.
An haife Lookman a Landan, an kuma amince ya bugawa Nijeriya kwallo ne bayan an yi duba kan asalin iyayensa.
Watakila ya ya fara bugawa Super Eagles wasa a wata mai kamawa, a wasan da Nijeriya za ta buga na share fagen cin kofin duniya da za a yi a Qatar.
Ya buga wa Ingila wasa a matakin ‘yan kasa da shekaru 19 da na 20 da kuma na 21, yana cikin tawagar Ingila da ta lashe kofin duniya na ‘yan kasa da shekara 20 a South Korea.
Victor Moses
Tsohon dan wasan gaban Chelsea na cikin tawagar Nijeriya da suka lashe gasar cin kofin Afrika a 2013 wadda aka yi a Afrika ta Kudu.
Kafin wannan lokacin, ya wakilcin Ingila a gasar ‘yan kasa da shekara 16 da 17 da 19 da 21.
Ba a kira Moses ba zuwa babbar tawagar Ingila, abin da ya bai wa Nijeriya damar kiran shi a watan Maris 2011 domin ya buga musu wasa da Habasha da Kenya.
Kafin ya sanar da daina kwallonsa a 2018, dan wasan ya buga wa Najeriya gasar 2014 da aka yi a Brazil da 2018 da aka yi a Rasha.
Alex Iwobi
Iwobi ya nuna alkawari lokacin da yake bugawa Ingila kwallo a mataki daban-daban.
Dan wasan ya fara shiga cikin tawagar Super Eagles ne a 2015.
A 2016, ya nuna kwarewarsa ga kungiyar lokacin da ya sauya Ahmed Musa a ranar 8 ga watan Oktoba a minti na 57 a wasan sada zumuntar da suka yi da DR Congo a Belgium.
Tsohon dan wasan na Arsenal da yanzu yake Everton, a shekaru bakwan da ya kwashe yana kwallo ya buga wasa 55 ciki har da na gasar Afcon da ya halarta sau biyu da kuma na cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018.
Shola Ameobi
Dan wasan gaban na daya daga cikin mutane kalilan da suka bugawa Najeriya wasa duk da cewa ya buga wa wata kasar tsallake wasanni a matakin yarinta.
An haife shi ne a Zaria da ke arewacin Nijeriya, sun koma Ingila da iyayensa lokacin yana dan shekara biyar a duniya.
A can, ya wakilci Ingila a gasar ‘yan kasa da shekara 20 tsakanin shekarar 2000 zuwa 2003.
Kazalika, Masu zaben ‘yan wasa a tawagar Najeriya sun dakko shi ne saboda kokarin da yake yi a Newcastle United – inda suka buga kwallon a zo a gani da Alan Shearer.
Bayan dogon jiran da ya yi Ingila ta kira shi ya yanke shawarar ya bugawa Najeriya wasa a 2011.
A 2013, ya fara buga wasa a wasan da Nijeriya ta yi da Malawi na samun gurbi a gasar kofin duniya.
Yana kuma cikin tawagar Stephen Keshi da ta halarci Brazil a 2014.
Ola Aina
Dan wasan gefe wanda ya taimaka wa matasan Chelsea suka lashe gasar Uefa ta matasa – an kira shi ya bugawa Nijeriya kwallo a karon farko cikin shekarar 2017.
Gabanin nan, Aina ya sanya rigar Ingila a matakin ‘yan kasa da shekara 16 da 17 da 18 da 19 da kuma 20 duka a tsakanin 2011 zuwa 2016.
Dan wasan Torino ya samu kyautar tagulla a Afcon a 2019 da aka yi a Masar – wata girmama ta hukuncin da ya yanke ya bar Turai domin sanya wa kasar Afrika riga.
A 2021 ya taka rawar a gani a Afcon karkashin Augustine Eguavoen, sai dai ba su yi nisa ba an cire su a matakin ‘yan 16.
