News
DA ƊUMI-ƊUMI: ASUU sun tafi yajin aiki
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Bayan kwashe awanni ta na tattaunawa a kan yadda za ta ɓullo wa lamarin rikicin ta da Gwamnatin Taraiya, Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa, ASUU, ta yanke shawarar tafiya yajin aikin gargaɗi na tsawon wata ɗaya.
Wata majiya a zaman tattaunawar da ASUU ta yi a Jihar Legas ta shaidawa jaridar Vanguard cewa ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki ne domin ta matsawa gwamnati lamba ta yi abin da ya dace.
Majiyar ta ƙara da cewa idan har gwamnati ba ta saurari bukatunta ba bayan wata ɗaya, to babu makawa ASUU za ta tsunduma yajin aiki na sai-baba-ta-gani.
Majiyar ta ce ta na so ta baiwa gwamnatin taraiyar dama ne ta gyara harkar ilimin jami’a wanda ya nufi hanyar durƙushewa.
“Mu ma iyaye ne. Mu na da ƴaƴa a makarantun jami’o’i a ƙasar nan, amma ba za mu bari a rusa ilimin jami’a ba.
” Mu mu na wannan fafutukar ne domin amfanin al’umma baki ɗayaɗaya. Idan a ka gyara tsarin to kowa zai amfana,” in ji majiyar.