Connect with us

News

Ban san ranar da za’a cimma matsaya da ASUU ba – Ministan Ilimi

Published

on

FB IMG 1645044026585
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, a ranar Larabar ya ce a shirye ya ke ya cimma matsaya da malaman jami’o’in da ke yajin aiki a karkashin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) sai dai ya ce bai san ranar da za’a kammala cimma matsaya ba

Yayin da yake ci gaba da kudurin cimma matsaya da kungiyar, Adamu ya yi imanin cewa a ko da yaushe akwai mafita kan kowace matsala.

“Akwai mafita kan hakan; tattaunawar ita ce mafita, “ ASUU Sun gabatar da yarjejeniya wanda ma’aikatar ke dubawa”. Inji shi

Advertisement

“Wani kwamiti yana dubansa. Gwamnati na kokarin ta sanar da abin da ta karɓa. Sai kwatsam muka ji sun tafiya yajin aiki. Muna son a yi sulhu cikin lumana.”

Ministan ya kuma mayar da martani kan wasu zarge-zargen da kungiyar ta ASUU ke yi, ciki har da ikirarin cewa ya na watsi da taron tattaunawa amma yana tura wakilai.

A maimakon haka, Adamu ya ce shi ne yake kiran duk wani taro, kuma ya kasance yana halarta sai dai ba halacci zaman na kwanan nan ba saboda ya kasance daidai da lokacin da ya je jinya a Jamus.

Advertisement

Ya kara da cewa zargin da ake yi na cewa gwamnati ba ta son a sasanta rikicin ba gaskiya ba ne.

Da aka tambaye shi ko gwamnati za ta cimma yarjejeniya da ASUU kafin karshen yajin aikin na kwanaki 30, ministan ya ce bai sani ba.

“Ba zan iya ba ku lokaci ba,” in ji ministan. “A shirye nake na cimma yarjejeniya da ASUU a yanzu, amma tunda ba ni kadai ba, ba zan iya ba ku lokaci ba. Amma tabbas za mu cimma yarjejeniya nan ba da jimawa ba.”

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *