Connect with us

Sports

Ahmed Musa ya baiwa tsohon ɗan wasan Super Eagles tallafin N2m

Published

on

FB IMG 1645106589746
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

Kaftin ɗin Tawogar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa, Super Eagles, Ahmed Musa ya baiwa tsohon ɗan wasan ƙasar, Kingsley Obiekwu tallafin Naira Miliyan 2.

A lokutan bayan ne dai Obiekwu, wanda da shi Nijeriya ta lashe gasar’Olympic’ ta ‘Atalanta 96’, ya baiyana cewa ya na fama da matsin rayuwa, inda motar shi kwaya ɗaya tak ya ke haya da ita domin ya kula da iyalinsa.

Tsohon ɗan wasan, wanda ya buga a Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Rangers International da ke Enugu da Udoji United, ya ce ya shiga harkar hayar mita ne sabo da matsin rayuwa.

Advertisement

Hakan ne ya sanya Ahmed Musa ya tausaya masa, inda ya bashi tallafin Naira Miliyan 2.

Ƴan Nijeriya da dama ne su ka riƙa godewa da yaba wa Ahmed Musa ta kafafen sadarwa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *