Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Pogba, Lingard, Ndombele, Eze, Raphinha, Schar, Ndidi

Published

on

0 GettyImages 1238510913
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

Ɗan wasan Faransa mai shekara 28 da ke buga tsakiya Paul Pogba, a shirye yake ya karbi tayi daga kungiyoyin firimiyar Ingila idan kwantiraginsa ya kawo karshe a wannan kaka a Manchester United(Telegraph)

Newcastle na shirin gabatar da sabon tayin £45m kan ɗan wasan Crystal Palace mai shekara 23 Eberechi Eze. (Mirror)

Advertisement

Jesse Lingard na Manchester United na iya watsi da bukatar komawa Tottenham a karshen kaka, ganin da alama dan wasan na Ingila mai shekara 29 ya fi son ya koma ketare. (Express)

Shugaban ƙungiyar Lyon Jean-Michel Aulas ya sanar da cewa mai yiwuwa su nemi ɗan wasan Faransa mai buga tsakiya Tanguy Ndombele a matsayin aro dagaTottenham. (RMC Sport, via Standard)

Ɗan wsan Brazil Raphinha da ke taka leda a Leeds Unitedda kuma ake alankatawa da Liverpool, ya ki aminta da sabon kwantiragin da aka sabunta masa. (Liverpool Echo)

Advertisement

Kocin rikon kwarya Ralf Rangnick ya yi cinikin farko kan ɗan wasa a Manchester United – bayan ya shaidawa Brandon Williams mai shekara 22 cewa zai koma Old Trafford idan wa’adin zaman aron sa ya cika a Norwich. (Sun)

Amma Manchester United na iya watsi da kokarin Rangnick lura da yadda ta datse cinikin ɗan wasan RB Leipzig mai shekara 24 Christopher Nkunku. (Bild, via Express)

Arsenal ta kasance kungiyar firimiya a baya-bayanan da ke nuna ta kwadaitu da ɗan wasan AC Milan’s mai shekara 22 Rafael Leao. (La Repubblica, via Metro)

Advertisement

Newcastle na fuskantar karan-batta a ci gaba da rike ɗan wasanta Fabian Schar da kwantiraginsa ke shiga wa’adin karshe, kungiyoyin AC Milan, Sevilla da Valencia na zawarcinsa. (Mail)

Brendan Rodgers ya ce dan wasan Leicester City Wilfred Ndidi darajarsa ta haura £50m bayan wasu labarai na alakanta Aston Villa da kokarin saye ɗan wasan asalin Najeriya mai shekara 25 a wannan kakar. (Birmingham Mail)

Manchester United ta kwadaitu da batun saye ɗan wasan nan mai shekara 21 asalin Barzil da ke taka leda a AjaxAntony. (90min, via Express)

Advertisement

West Ham ta bi sahun Leeds a farautar ɗanw asan Huddersfield mai shekara 23 Lewis O’Brien. (Teamtalk

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *