News
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Zamfara ya rasu a haɗarin mota

Daga yasir sani abdullahi
Kwamishina a Hukumar Zaɓe ta Jihar Zamfara, ZASIEC, Hashimu Gazura ya rasu a wani mummunan haɗarin mota.
Gazura ya rasu a jiya Juma’a.
Kanfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa Gazura tsohon ɗan majalisar jiha ne mai wakiltar Mazaɓar Gummi 2.
Mansur Bagudu, Shugaban Hukumar kula da Harkokin Majalisar Dokoki ta Jiha ne ya sanar da rasuwar a wata sanarwa a yau Asabar.
Ya ce ya rasu ne a wani mummunan haɗarin mota a kan hanyar Yawuri a Jihar Kebbi a ranar Juma’a.
Tun misalin 11 na safiyar yau ne dai a ka yi jana’izar Gazura a fadar Sarkin Gummi.