Connect with us

News

Almundahanar N73.7m: Kotu ta yanke wa tsohon babban akanta na Hukumar Alhazai shekara 7 a gidan yari

Published

on

FB IMG 1645289511800
Spread the love

Daga aminu usman jibrin

 

 

Advertisement

 

A ranar 16 ga watan Febrairu ne a ka yanke wa tsohon babban akanta na Hukumar Alhazai Musulmai ta Jihar Bauchi, Kawu Chindo, da wani ma’aikacin ofishin Akanta-Janar na jihar, Ali Baba, hukuncin shekaru bakwai da wata uku a gidan yari.

Mai Sharia Mu’azu Abubakar na Babbar Kotun Jihar Bauchi ne ya yanke musu hukuncin bayan da Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC ta yankin Jihar Gombe ta ka kama su da laifuka biyar da su ka haɗa da haɗin baki da kuma yin sojan-gona.

Advertisement

Ma’aikatar Kuɗi da Ci gaban Tattalin Arziki ta jihar ce ta kama su biyun da laifin da fitar da shaidar biyan kuɗi da rasiti na bogi a matsayin shaidar biyan kuɗin Hajji na 2019 ga maniyyata.

Haka kuma an kama su da laifin ƙin saka N73, 715,286.62 a asusun Hukumar Hajji ta Jihar Bauchi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *