News
Waɗanda su ke da bizar yawon buɗe ido da ta kasuwanci ba za su yi aikin hajji bana ba — Saudiya
Abubakar musa
Hukumar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta fitar da rukunin waɗanda ba ƴan Saudiya da ba za su yi aikin Hajjin 2022 ba.
A wata sanarwa da Hukumar ta fitar a jiya, waɗanda su ke da bizar da a ka saba yi idan za a shiga ƙasar, ko kuma mazauna ƙasar da su ke da shaidar iznin zama me kaɗai ne za su yi aikin Hajji.
Hukumar ta ce nan gaba kaɗan za ta sanar da shirye-shirye da tsare-tsare na aikin Hajjin bana ta sahihan kafafen ta na sadarwa.
A tuna cewa a bara, mahajjata 60,000, kuma mazauna Saudiya ne su ka yi aikin Hajji, kuma sai da a ka yi wa kowa allurar rigakafin korona karo biyu-biyu.