News
A shirye muke mu kwato Najeriya daga hannun APC da jam’iyyar PDP – TNM
Daga yasir sani abdullahi
A ranar Talata ne tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana kafa runduna a karkashin inuwar kungiyar National Movement, inda hakan ya kara haskawa a siyasar Najeriya a zaben 2023.
A cewarsu, rundunar za ta karbi mulki daga hannun jam’iyyar All Progressives Congress a shekarar 2023.
TNM ta ce tana sane da kwakkwaran aikinta na ceto Najeriya daga wargajewa.
Da yake jawabi a wajen taron, wanda ya shirya taron, Kwankwaso, ya ce burinsu na hada kai ne na ceto kasar nan.
“Tun da dadewa ‘yan Najeriya suna jiran wannan rana. Abokan ƴan Najeriya da ke waje sun daɗe suna jiran wannan rana kuma lokaci ya yi yau.
“A yau, duk ‘yan Nijeriya sun taru a anan, Kudirinmu ne na ganin mun ceto al’ummarmu daga wannan mawuyacin hali.”
“Kungiyar ta kasa tana da mambobi a kowace karamar hukuma da wajen kasar nan,” in ji Kwankwaso..
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
