News
Kasuwar ƴan ƙwallo: Madrid na zawarcin Pochettino, City na son Silva, makomar De Gea da Mbappe
Muhammad Muhammad zahraddin
Real Madrid za ta bi sahun Manchester United wajen neman kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino. (Mail)
Dan wasan Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 27, na sa ran komawa Real Madrid. (CalcioMercato)
Liverpool na matukar sha’awar sayen dan wasan gaban Ingila Jarrod Bowen, mai shekara 25, daga West Ham. (GiveMeSport)
Inter Milan tana sa ido kan dan wasan Manchester City dan kasar Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 24 (CalcioMercato)
Kocin Leicester Brendan Rodgers yana samun goyon bayan hukumar kulab din duk da rashin tabuka komai. (Telegraph)
Chelsea na zawarcin dan wasan bayan Wolves dan kasar Ingila Max Kilman, mai shekara 24. (Talksport)
Liverpool ta fita daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 23, daga Paris St-Germain. (Sports)
Arsenal, da Newcastle, da Borussia Dortmund da Inter Milan na zawarcin dan wasan gaban Lille da Canada Jonathan David, mai shekara 22. (TuttoMercatoWeb)
Tottenham za ta jira ta fara tattaunawa da dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 28, kan sabon kwantaragi. (Sports)
Golan Manchester United da Spain David De Gea, mai shekara 31, ya ce a shirye yake ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da kungiyar. (Independent)
Dan wasan tsakiya na Ingila Jonjo Shelvey, mai shekara 29, da dan wasan baya na kasar Switzerland Fabian Schar, mai shekara 30, na gab da sanya hannu kan sabbin kwangiloli a Newcastle. (Telegraph)
Roy Keane, mai shekaru 50, ya ki amincewa da damar zama kocin League One Sunderland saboda kawai sun ba shi kwantiragin watanni shida kuma yana son karin lokaci. (Sun)
Roma ba za ta ci gaba da rike Ainsley Maitland-Niles n Arsenal da ke tare da ita a matsayin aro ba, saboda bai taka rawar gani a Seria A ba (Calciomercato)
Wembley za ta iya karbar bakuncin wasan karshe na gasar zakarun Turai na bana idan Uefa ta yanke shawarar hana buga wasan a St Petersburg saboda rikicin Rasha da Ukraine. (Mirror)
Fatan Newcastle, da Leeds da Crystal Palace na sayen dan wasan tsakiya na Wales Brennan Johnson, mai shekara 20, ya lalace, inda Nottingham Forest ke kara kokarin ganin ya sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya. (Mirror)
