Gobara ta tashi a hedikwatar ma’aikatar kuɗi ta Najeriya da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Babu tabbaci kan ko me ya jawo gobarar sai dai tuni ma’aikatan kashe gobara suka isa wurin.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun hukumar kashe gobara wato Abraham Paul inda ya ce ma’aikatansu na can suna ƙoƙarin kashe wutar.