News
Asalin rikicin ƙasar Rasha da Yukren: Shin ko mene ne ne alaƙar NATO da rikicin?

Daga yasir sani abdullahi
Kafar yaɗa labarai ta BBC ta samar da bayanai game da asalin wannan rikici wanda har ya kai ga zub da jini a tsakanin ƙasashen Turai da ake jin cewa sun gama wayewa. To amma sai ga shi a yau sun ɗebo makaman ƙare dangi suna kashe junansu.
BBC ta kawo rahoto kamar haka:
“Mece ce kungiyar Nato kuma me ya sa Rasha ba ta yarda da ita ba?
Kasashen da ke cikin kungiyar Nato na nazari su ga irin matakin da za su iya dauka na taimaka wa Ukraine yayn da Rasha ke neman mamayarta.
Kawancen wanda ya kunshi Amurka da Birtniya da Faransa da Jamus yana kara shiri da taimako na soji domin taimak wa Ukraine
Mece ce ƙungiyar Nato?
Nato – Kungiyar tsaro ce me hadakar sojojin kasashen yankin Arewacin Atalantika, wadda kasashe 12 da suka hada da Amurka da Kanada da Birtaniya da Faransa suka kirkiro a 1949.
Kasashen sun yi alkawarin kai wa duk daya daga cikinsu da ke fuskantar wata barazanar tsaro taimako.
Da farko manufarta ita ce ta kalubalanci duk wani yunkuri na mamaya ko fadadar da Rasha za ta nemi yi bayan yaki a Turai.
A 1955 Rasha ta lokacin Tarayyar Soviet ta mayar da martani ga kirkirar ta Nato, inda ita ma ta kirkiro hadakar soji ta kasashen kwaminishanci na Gabashin Turai, kawancen da ta sanya wa suna Warsaw Pact.
Sakamakon rushewar Tarayyar Soviet a 1991, wasu daga cikin kasashen da ke cikin kawancen na Rasha ( Warsaw Pact), sai suka koma kungiyar Nato inda ta zama da mambobi 30 yanzu.
Me ya haddasa saɓanin Rasha da Nato da Ukraine a yanzu?
Ukraine kasa ce ta rusasshiyar Tarayyar Soviet, wadda ke da iyaka da Rasha da kuma Tarayyar Turai.
Ba mamba ba ce ta Nato, amma ƙawa ce; wannan na nufin akwai fahimtar juna da cewa za a iya barinta ta shiga kungiyar ta nan gaba.
To ita kuwa Rasha tana adawa da hakan saboda haka ne take son ta samu tabbaci daga ksashen yamma cewa hakan ba za ta taba kasancewa ba, wanda kuma wannan abu ne da su kuma kasashen yamma ba za su yi ba.
To ita kuma Ukraine kasa ce da ke da ‘yan kabilar Rasha da yawa sannan kuma kasa ce da ke da alaka ta tarihi da dangantaka da Rasha. A takaice ma dai Rasha na daukarta kamar bayan gidanta.
Mene ne kuma Rasha ta damu da shi?
Shugaba Putin ya ce kasashen yamma sun yi amfani da kawancensu na Nato sun kewaye Rasha, saboda haka yake son kungiyar ta daina ayyukan da take yi na soji a Gabashin Turai.
Ya dade yana cewa Amurka ta karya alkawarin da ta yi a 1990 cewa Nato ba za ta fadada ba zuwa Gabashin Turai.
Nato ta yi watsi da iikirarin na Rasha da cewa wasu mambobinta kadan ne kawai suke da iyaka da Rashar, kuma kawance kawai na tsaro.
Mutane da dama suna ganin dakarun da Rasha take ta girkewa a kusa d iyakarta da Ukraine wata dabara ce ta tilasta wa kasashen yamma su dauki bukatar ta Rasha da muhimmanci.
Me Nato ta taɓa yi a baya a kan Rasha da Ukraine?
Lokacin da ‘yan Ukraine suka hambarar da shugaban ƙasarsu mai ra’ayin Rasha a farko-farkon 2014, Rasha ta mamaye tsibirin kudncin Ukraine, Crimea.
Haka kuma ta goyi bayan ‘yan aware masu masu ra’ayin Rasha wadanda suka kama yankuna da dama na Ukraine.
Nato ba ta shiga rikicin ba, amma ta mayar da martani ta hanyar girke dakaru a kasashen gabashin Turai da dama a karon farko.
Tun bayan da Rasha ta mamaye Crimea, Nato ta zube dakaru a gabashin Turai
Tana da dakarun hadin guiwa na kasashe hudu wadanda yawansu ya kai rundunar yaki a Estonia da Latvia da Lithuania da kuma Poland da kuma wata rundunar da hadakar kasashe a Romania.
Haka kuma ta fadada aikin sanya ido na tsaro ta sama a kasashen yankin Baltic da gabashin Turai domin tare duk wani jirgin saman Rasha, wand ya keta iyakar kasashe mambobinta.
Rasha dai ta ce tana son ganin fitar wadannan sojoji, su bar yankin gaba daya.
Wane yunkuri Nato ta yi a kan Ukraine?
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Rasha za ta ɗanɗana kuɗarta idan ta yi mamaya.
Amurka ta jibge sojojinta 8,500 da ke cikin shirin yaki, to amma kuma ma’aikatar tsaron Amurkar ta ce za a tura su fagen daga ne kawai idan Nato ta yanke shawarar tura dakarunta na kan-ta-kwana
Ta kuma kara da cewa ba ta da wata niyya ta tura dakaru Ukraine ita kanta.
Ministar harkokin waje ta Jamus Annalena Baerbock ta yi gargadin cewa duk wani mataki na soji da Rasha ta kuskura ta kara dauka to za ta dandana kudarta ta fannin tattalin arziki da siyasa da kuma wasu hanyoyi.
Gwamnatin Birtaniya ta ce kasar ta amince cewa, dole ne kawaye wato Nato su kwana da shirin daukar matakin gaggawa na martani wanda ya hada da jerin takunkumin da ba a taba gani ba
Shin Nato ta hada kai ne a kan Ukraine?
Shugaba Biden ya ce akwai cikakken hadin kai da shugabannin Turai, amma kuma akwai sabani a kan irin taimakon da kowace kasa ta ce za ta bayar.
Amurka ta ce ta tura tan 90 na taimakon makamai da suka hada da harsasai zuwa Ukraine domin amfanin dakarun kare fage. Birtaniy kuwa na aika wa Ukraine din makamai masu linzami da kecin gajeren zango masu tarwatsa igwa.
Wasu mambobin Nato da suka hada da Denmark da Sifaniya da Faransa da Holland na tura jiragen yaki na sama da na ruwa zuwa gabashin Turai domin karfafa tsaro a yankin.
Sai dai Jamus ta ki amincewa d bukatar Ukraine ta tura mata makaman kariya, saboda manufarta ta hana tura makamai masu lahani wuraren rikici. A mimakon haka za ta tura taimakon kayan kula da lafiya ne.
Shugaba Macron na Faransa shi kuwa yana kira ne da a zauna a tattauna da Rasha domin yayyafa wa wutar rikicin ruwa.