Connect with us

News

UEFA ta dage wasan karshe na Champions League daga Russia zuwa Faransa

Published

on

Screenshot 20220226 064148
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA ta dage wasan karshe na maza na gasar cin kofin zakarun turai Champions League na shekarar 2021/2022 daga kasar Russia zuwa Faransa.

Hakan na zuwa ne bayan wani zama da masu ruwa da tsaki na hukumar suka gudanar a ranar Juma’a 24 ga Fabrairun 2022 da muke ciki.

Advertisement

UEFA ta ce dage wasan ya biyo bayan yadda matsalar tashin hankali ke ci gaba da wakana tsakanin Russia da Ukraine.

Wasan karshen dai an tsara gudanarwa a birnin Saint Petersburg, wanda kawo yanzu za a gudanar a filin Stade de France da ke kasar Faransa a ranar Asabar 28 ga Mayun 2022.

Zuwa yanzu dai ana ci gaba da musayar wuta tsakanin kasashen Russia da Ukraine da sakamakon haka ake ci gaba da dage wasanni da dama a kasashen biyu.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *