Connect with us

News

OIC ta yaba wa Buhari bisa kyautar dala miliyan 1 da ya baiwa Afghanistan

Published

on

FB IMG 1646370556169
Spread the love

Daga khadija abdullahi Muhammad

 

 

Ƙungiyar Haɗin kan Musulmi, OIC, ta yaba wa Gwamnatin Taraiya bisa gagarumar kyautar da ta baiwa Gidauniyar Tallafin Jinƙai ta Afghanistan.

Advertisement

Sakatare-Janar na OIC ɗin, Hissein Brahim Taha ne ya yi yabon a wata sanarwa da shelkwatar ƙungiyar ta aike wa jaridar Daily Nigerian a yau Alhamis.

Sanarwar ta ce tallafin ya zo a daidai lokaci domin kungiyar ta samu damar ƙara aiyukan jin kai da a ke yi a Afghanistan.

Sanarwar ta ƙara da cewa Tallafin kuɗin zai taimaka a tallafa wa miliyoyin mutane maza da mata da ƙananan yara a Afghanistan.

Jaridar indaranka tuna cewa a watan Disamba 2021 ne OIC ta kaddamar da Gidauniyar tallafin domin magance wahalar da al’umma su ke sha a Afghanistan a wani babban taro da ta haɗa.

Advertisement

Haka zalika Nijeriya ita ma mamba ce ta OIC din kuma na ɗaya da ga cikin ƙasashen da suka sanar da tallafin.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *