Connect with us

News

ASUU Ta Umarci ABU Da Ta Kwace Digirin Da Ta Ba Gwamna El Rufai A 1980.

Published

on

FB IMG 1646370918058
Spread the love

Daga mujahid dallami garba

 

 

Advertisement

 

Kungiyar malaman jami’a na reshen jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta yi kira ga shugabannin jami’ar da su karbe digirorin Nasir El-Rufai.

Rahoto ya fito daga jaridar Abusites cewa kungiyar ASUU ta cin ma matsaya cewa a raba Malam Nasir El-Rufai da shaidar karatun da ya samu a jami’ar tun a 1980.

Advertisement

Hakan na zuwa ne bayan sabanin da aka samu tsakanin mai girma gwamnan na jihar Kaduna da shugabannin jami’ar ABU Zaria game da batun wani fili.

Kungiyar ta ce abubuwan da gwamnan na Kaduna yake yi, sun ci karo da koyarwa da tarbiyar da ya samu daga wannan babbar jami’a mai dadadden tarihi.

ASUU ta cin ma wannan mataki bayan zaman da tayi a Samaru Zaria a ranar Laraba, 2 ga watan Maris 2022, a karkashin jagorancin Farfesa Haruna Jibril.

Advertisement

Sabon shugaban ASUU da sakatarensa a ABU Zaria, Haruna Jibril da Husseini Abdullahi su ka sa hannu a takardar da aka fitar bayan wannan zaman a jiya.

Takardar tana cewa malaman jami’ar sun tattauna a kan batun yunkurin gwamna Nasir El-Rufai na karbe filin ABU da karfi da yaji, duk da kotu ta hana shi.

Rahoton ya ce ASUU ta tsaida magana cewa za ta je kwalejin aikin gona da gandun dabbobin da ke unguwar Mando ta shirya zanga-zanga domin nuna jin dadinta.

Advertisement

Tun a watan jiya aka ji cewa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria za ta sake shigar da karar Gwamnatin Nasir El-Rufai a kotu saboda zargin saba umarnin Alkali.

Duk da mai shari’a K. Dabo ya ce ka da kowa ya taba filin, sai aka ji jami’an KASUPDA sun yi watsi da umarnin kotu, sun fara ruguza filin DAC da ke Mando, garin Kaduna.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *