News
Majalisa Ta Yi Watsi Da Kudurin Hana Jami’an Gwamnati Tura ‘Ya’yansu Karatu Waje.
Daga yasir sani abdullahi
Yan majalisar wakilai a ranar Alhamis, 3 ga watan Maris, sun yi watsi da kudirin dokar da ke neman hana jami’an gwamnati tura ‘ya’yansu makaranta zuwa kasashen ketare.
Wasu daga cikinsu sun dage kan cewa hakan ya saba wa muhimman hakkokin ‘yan Najeriya.
Kudirin dokar na Sergius Ogun, ya nemi a tabbatar da cewa jami’an gwamnatin da za su iya nuna cewa za su iya daukar nauyin ‘ya’yansu a kasashen waje ba tare da amfani da kudin gwamnati ba ne kadai za su iya hakan.
‘Yan majalisar sun roki Mista Ogun da ya janye kudirin amma ya ki, kuma da aka kada kuri’a, sai akasarin kuri’un suka nuna kin amincewa da kudirin.
Daga karshe, kudurin da ke neman sauya sashe na 46 a kundin kiwon lafiya ya sha kaye a majalisa bayan dogon caccaka tsinke daga nan aka yi watsi da shi.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
