News
2023: Ba zan yarda da yawo da makamai da dabanci ba, Ganduje ya gargaɗi ƴan siyasa
Daga mujahid danllami garba
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ja kunnen ƴan siyasa a jihar nan da su guji amfani da makamai a wuraren tarukan siyasa.
Gwamnan ya yi jan kunnen ne yayin da ya jagoranci ƙaddamar da sabbin zaɓaɓɓun Shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar Kano ta arewa, wanda ya gudana a Ƙaramar Hukumar Bichi a jiya Talata.
Gwamna Ganduje ya ce amfani da makamai a wuraren tarukan siyasa bai dace a riƙa ganin hakan da ga ƴan siyasa masu manufa ba, waɗanda kamata ya yi su mai da hankali wajen inganta rayuwar al’ummar su ba lalata rayuwar matasa ba.
Yace Jam’iyyar APC a Kano ba ta da burin da ya wuce inganta rayuwar al’umma, usamman mata da matasa domin su ne kashin bayan cigaban kowacce irin al’umma.
Ganduje ya kuma buƙaci sabbin Shugabannin jam’iyyar da su mai da hankali wajen shiga lungu da saƙo na yankunansu don su wayar musu da kai, su fahimci aiyukan alkhairi da jam’iyyar ta gudanar a tsahon shekaru 8 da su ka gabata a ƙasar nan.