News
DA ƊUMI-ƊUMI: Sakataren APC na ƙasa ya yi murabus

Daga yasir sani abdullahi
Rikicin jam’iya mai mulki ta APC ya ƙara ta’azzara bayan da Sakataren riƙo na jam’iyar na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe ya ajiye muƙaminsa.
Jaridar The Nation ta jiyo cewa Sakataren ya mika takardar ajiye aikin nasa ne ga sabon shugaban kwamitin riƙo na jam’iyar, Gwamna Abubakar Sani Bello yayin ganawa ta kullum-kullum a Sakateriyar jam’iyar a yau Talata.