Sports
Kasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Lukaku, Jorginho, Emerson, Alonso, Azpilicueta, Salah
Daga Khadija Ibrahim Muhammad
Ɗan wasan Chelsea Romelu Lukaku mai shekara 28, a shirye ya ke ya amince a azabtare masa albashi domin bashi damar ya koma zaman aro a Inter Milan.(Calciomercato – in Italian)
Lukaku ya nuna takaci da yada wasu ke ganin ya yanke wannan hukunci ne saboda halin da Chelsea ta tsinci kanta, yana mai cewa ba shi da niyyar bankwana da kulob din baki daya a yanzu. (Telegraph – subscription required)
Juventus na farautar yan wasan Chelsea biyu – mai buga tsakiya Jorginho ɗan shekara 30 da ɗan wasan baya Emerson Palmieri mai shekara 27, wanda yanzu haka ke zaman aro a Lyon. (Tuttosport – in Italian)
Barcelona na sanya ido kan halin da Chelsea ke ciki inda take nuna zawarcinta kan ‘yan wasan Sifaniya Marcos Alonso da Cesar Azpilicueta da kwantiraginsa ke ƙarewa a kakar bana. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Kafar yaɗa labarai a Saudiyya ta gabatar da tayin saye Chelsea da kuma shirinta na sake sauya tsari a Stamford Bridge da sabunta kwantiragin ‘yan wasa irinsu Azpilicueta da Antonio Rudiger na Jamus wanda kwantiaginsa ke gab da karewa. (Goal)
Dan wasan gaba a Masar Mohamed Salah mai shekara 29, na son ci gaba da zama a kungiyar Firimiya ko da ya gaza amincewa da sabon kwantiraginsa a Liverpool. (Football Insider)
Manchester United ta shiga sahun masu fafutika kan ɗan wasan Real Sociedad Alexander Isak na Jamus mai shekara 22. (Star)
Mai horar da Paul Pogba ya ce ɗan wasan na Fransa zai bar Manchester United idan kwantiraginsa ya ƙare a kakar bana. (Calciomercato – in Italian)
Newcastle na tattaunawa da ɗan wasan Ingila mai buga tsakiya Sean Longstaff, wanda kwantiraginsa ke ƙarewa a bana, kan sabon kwangila mai tsayi. (Times)
Manchester United na iya kokarta dawo da Sam Johnstone daga West Broma wannan kakar, duk da cewa Tottenham da Southamptonduk sun nuna sha’awara gwada sa’arsu kan matashin ɗan wasan mai shekara 28. (Sun)
Chelsea za ta yi amai ta lashe kan sayo ɗan wasan Sifaniya mai buga tsakiya Saul Niguez daga Atletico Madrid a wannan kakar- idan takunkuman gwamnatin Burtaniya sun bata dama. (Mirror)
Chelsea ta roƙi gwamnatin Burtaniya ta dage mata takunkumi domin tsawaita kwantiragin ‘yan wasanta, yayin da ake fargabar babbar matsalar da za ta iya fadawa a sabuwar kaka. (Telegraph – subscription required)
Manchester United na zaman shirin yiwuwar iya saye kocin Chelsea Thomas Tuchel a karshen wannan kakar. (Mail)
Kocin Ajax Erik ten Hag ya shirya karban horas da Manchester United – kuma zai amince ya yi aiki tare da kocin riƙon ƙwarya Ralf Rangnick. (Mirror)
Real Madrid na son ci gaba da riƙe ɗan wasan Croatia mai buga mata tsakiya Luka Modric. (Marca – in Spanish)
AC Milan ta kai ga cimma yarjejeniya da Lille kan saye ɗan wasan tsakiya mai shekara 24 Renato Sanches a wannan kakar. (Calciomercato – in Italian)
Juan Mata na iya samun aiki horar da Manchester United– idan kwantoraginsa ya kare a wannan kakar. (Sun)
