Connect with us

News

Hulɗar Rasha da China za ta ƙara ƙarfi – Lavrov

Published

on

Daga Khadija Ibrahim muhammad

 

 

 

Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce hulɗar Rasha da China za ta ƙara ƙarfi duk da halin da ake ciki a yanzu.

“A lokacin da ƙasashen yammaci ke yi gani-gani kan tushen yadda tsarin ƙasa da ƙasa ya ginu akai, ba shakka – mu a matsayinmu na manyan ƙasashe biyu- muna buƙatar mu yi tunanin yadda mu ci gaba a wannan duniyar,” kamar yadda Mista Lavrov ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Rasha Interfax.

A wata zantawa ta wayar salula a ranar Juma’a, shugaban Amurka Joe Biden ya yi gargaɗi ga shugaban China Xi Jinping kan abin da zai biyo bayan ga China idan har ta taimakawa Rasha a yaƙin da take yi a Ukraine.

Advertisement

Kafofin yaɗa labaran China sun ruwaito cewa Xi ya bayyana yaƙin a matsayin abin da bai shafi kowa ba, amma ba tare da ya soki shugaba Putin ba kai-tsaye.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending