Connect with us

News

DA DUMI-DUMINSA| An Kadammar da Kwalejin Kiwon lafiya ta Musulunci a Ƙasar Ghana.

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

 

Maigirma Mataimakin Shugaban Kasar Ghana Dr Mahmud Bawumia ya gayyaci shugaban Kungiyar Izala na duniya Ash-sheikh Dr Abdullahi Bala Lau (H) tare da Sakataren kungiyar Izala Ash-sheikh Dr Muhammad Kabir Haruna Gombe (H)

Mataimakin Shugaban Kasar ya gayyaci Malaman zuwa Kasar Ghana domin su tattauna kan abinda ya shafi cigaban addinin Musulunci a nahiyar Afirka

Advertisement

Sannan an gayyaci Malaman zuwa kaddamar da sabuwar makarantar koyar da aikin kiwon lafiya wandanl aka saka mata sunan Musulunci wato Islamic Nursing Training School dake Kasar Ghana

Kamar yadda zaku gani a hoto, ginin Makarantar yana da bene uku, bene na farko an saka sunan Kakan Ahlussunnah a Nigeria, Alqadiy Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (Rahimahullah), a bene na biyu an saka sunan Sheikh Dr Kabir Haruna Gombe, a bene na uku an saka sunan Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau

Jagoran kungiyar Izala na duniya Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi alkawarin taimakawa wajen gudanar da wannan makaranta na Musulunci, sannan za’a dinga bada tallafin karatun kyauta a makarantar ma wasu dalibai masu kwazo

Izala ikon Allah ba na mutum ba!

Yaa Allah Ka daukaka darajar Musulunci da Musulmai a duk inda suke a duniya Amin

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending