Connect with us

News

Rasha ta ce ta kashe sojojin haya na ƙasashen waje a harin makami mai linzami

Published

on

Daga  Hamza Yusuf Abdulmumin

Advertisements
Advertisements

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta kashe sojojin haya da dama a harin makami mai linzami da aka kai a wata cibiyar horar da sojoji a yammacin Ukraine, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na RIA ya ruwaito.

Manjo Janar Igor Konashenkov, kakakin ma’aikatar, ya ce fiye da sojojin Ukraine 100 da “wasu sojojin haya” ne aka kashe a lokacin da “makami mai linzami” ya faɗa wani sansanin sojin Ukraine da ke kusa da Ovruch a Zhytomyr.

Advertisements

“Makamai masu linzami da aka harba ta sama sun kai hari a cibiyar horas da dakarun soji na musamman na Ukraine, inda sojojin haya na kasashen waje da suka isa Ukraine ke zaune,” in ji Konashenkov.

Advertisements
Advertisements

INDARANKA ba za ta iya tabbatar da wannan ikirarin ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending