Connect with us

Sports

Xavi: Ƙofar Barcelona a buɗe take ga Messi

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya ce ƙofar Barcelona a buɗe take Lionel Messi a duk lokacin da yake so ya dawo.

Xavi ya faɗi haka ne a taron manema labarai a ranar Asabar kan shirin da yake na haɗuwa da Real Madrid a La Liga a wasan hamayya na Clasico.

Messi ya koma PSG da taka leda bayan Barcelona ta ce ba ta iya sabunta kwangilar shi.

An tambayi Xavi ko zai iya dawo da Messi, sai kocin ya ce: “idan dai ni ne koci, ƙofa a buɗe take idan har yana son ya dawo a ko wane lokaci.”

Xavi ya kuma yi wa Messi tayin kawo ziyara domin kallon atisayen Barcelona , tare da tattaunawa da shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending