Sports
Barcelona ta yi fata-fata da Real Madrid
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
A fatawar gasar Laliga tsakanin Real Madrid da Barcelona, Barca ta bi Madrid har gida ta lallasa ta da 4-0 a wasa mai taken El Clasico.
Pierre Emerick Aubameyang ne ya fara jefa kwallo a ragar Madrid tun a minti na 29.
Kamar wasa, ashe cin da Aubameyang ya yi, ya karya asirin ragar Madrid me, inda a minti na 38, R. Araujo ya ƙara.
A minti na 47, jim kaɗan bayan dawo wa da ga hutun rabin lokaci, ai kuwa sai kwallon ta uku ta faɗa ragar Madrid ta hannun yaron nan mai tashe, Ferran Torres, inda daga bisani Aubameyang ya ƙara ƙwallo ta huɗu a minti na 51.
Wannan wata gagarumar nasara ce ga Barcelona, musamman ganin cewa ƙungiyar ta fara kakar bana da rashin kokari.
Sai dai kuma tuni Barcelona su ka fara farfaɗo wa a hannun sabon koci kuma tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Xavi Hernandez.
Da yawa sun zaci Madrid za ta doke Barcelona ganin yadda Madrid ɗin ke tashe, sai gashi Barca ta zamto ɗan hakin da ka raina…
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
