News
Wahalar man fetur ka iya kawo zanga-zangar datafi ta ENDSARS” -PDP ta fadawa Gwamnati
Daga maryam bashir musa
jam’iyyar PDP ta gargadi gwamnati cewa wahalar man fetur ka iya kawo zanga-zangar dafafi ta ENDSARS wacce akayi a watan oktoba na shekarar 2020.
Inda PDP ta kara da cewa yanzu litar futur ta kai 400-500, sannan kuma litar kananzir ya kai kusan naira 750 yayin da kuma diessel ya kai 670.
A makon daya gabata ranar talata mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina ya bayyana cewa Shugaban kasa ya bayyana bacin ransa akan wahalar man fetur kuma yace yana baiwa yan kasa hakuri bakidaya.
Advertisements
