Connect with us

News

Ga wasu abubuwan da muka wayi gari da su a mamayar da Rasha ke yi a Ukraine

Published

on

Idan yanzu ku ka fara bibiyar INDARANKA ga wasu muhimma abubuwan da suka faru kawo wayewar gari yau Talata a yakin da Rasha ke yi da ukraine:

Advertisements
Advertisements
  • Gargadin Biden: Shugaban Amurka ya ce akwai alamu bayyanannu cewa Vladimir Putin na shirin amfani da makamai masu guba a Ukraine. Biden ya kuma ce shugaban na Rasha “ba shi da wurin gudu” saboda turjiyar da Ukraine ke nunawa kan wannan yakin, kuma akwai hadarin zai iya fara amfani dawasu muggan makamai
  • Turjiyar Zelensky: Shugaban Ukraine ya ce kasarsa ba za ta taba mika wuya ga bukatun Rasha ba – wannan na zuwa ne bayan da Rashar ta ce za ta kyale mazauna birnin Mariupol su fice daga birnin idan Ukraine ta amince za ta mika ma ta birnin. Ya kuma sake yin kira da a tattauna kai tsaye tsakaninsa da Shugaba Putin “ta kowane hali” domin kawo karshen yakin
  • Rasha ta kara kai hare-hare ta sama: Dakarun Ukraine na cewa Rasha ta kara bude wuta ta hanyar amfani da jiragenta na yaki cikin sa’a 24 da ta gabata
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending