Connect with us

News

Makomar ruwa a Afirka:Kuna da fargabar ƙarewar ruwa nan gaba a birni da ƙasarku?

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM
 

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

Yayin da al’ummar duniya ke ƙaruwa, buƙatar ruwa mai kyau da tsafta kuma mai sauki na ƙaruwa ita ma, abin da ke sa matsi da raguwar ruwan da ake da shi. Wannan shi ne ake kira ”matsin ruwa”.

Zuwa shekara ta 2025, rabin al’ummar duniya za su kasance suna rayuwa a yankunan da ke fama da matsalar matsin ruwa, kmar yada Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.

Ba za a iya ci gaba da samar da ruwa mai daɗi ba daidai da buƙatar duniya da ke karuwa ba. Ba a samun ruwa daidai-wa-daida a fadin duniya, kuma zai kasance da matukar wuya a riƙa samo ruwa mai daɗi kuma zai yi tsada a rika safararsa.

Advertisement

Ƙaruwar jama’a da bunkasar birane da sauyin yanayi na daga cikin abubuwan da ke haddasa ƙarancin, ta hanyar rashin ruwan ko kuma gurɓata hanyoyin da ake da su na samun ruwan.

Bari mu mayar da hankali a kan Afirka

Zuwa shekara 30 nan gaba an yi hasashen yawan al’ummar Afirka zai ninka biyu zuwa biliyan 2 da rabi in ji Ƙungiyar Hadin kan Tattalin Arziki da Ci-gaba (OECD).

Tuni daman rabin al’ummar Afirka na zaune ne a birane, kuma sama da rabinsu suna zaune ne a unguwanni na talakawa.

Ƙwararru sun yi gargagaɗin cewa matukar ba a ɗauki mataki ba mutane sama da miliyan ɗari daya a birane za su fuskanci matsanancin ƙarancin ruwa.

Afirka ce nahiya mafi ƙarancin ruwa a duniya. Kusan biyu bisa uku na sararinta ko dai mai karancin ruwa ne ko kusa da haka.

Ɗaya daga cikin mutum uku a yankin Afirka kudu da hamadar Sahara na rayuwa ne a wurin da ake fama da ƙarancin ruwa.

Eritrea da Botswana na daga cikin ƙasashen Afirka da dama da ke fama da matsalar ruwa.

Advertisement

Manyan matsalolin wadatar ruwa

Sauyin yanayi na haddasa yanayi da ba za a iya hasashe ba da ya hada da fari da ambaliya. Kyawun ruwan da ake samu daga ƙarkashin ƙasa ya ragu a yankuna da yawa

Ana asarar miliyoyin ranaku na aiki da nazari a kowa ce sheakara saboda rashin lafiya wadda rashin ruwa ko rashin kyawunsa ke haddasawa

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending