Connect with us

News

DLEA ta kama ƙwayar Tramadol miliyan biyu a Legas

Published

on

Daga maryam Bashir musa

 

Hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ce ta kama ƙwayar Tramadol kusan miliyan biyu tare da maganin tari na Codeine a filin jirgin sama na Muratala Muhammad da ke Legas.lllll

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Laraba ta ce an shigar da ƙwayoyin ne daga Pakistan da kuma Birtaniya.

Ta ƙara da cewa an ƙwace kayan a ranar 10 ga watan Maris, inda aka samu ƙwaya samfurin Co-codamol 349,800 wadda gwamnati ta haramta.

Sai kuma a ranar 15 ga Maris, inda jami’an NDLEA tare da haɗin gwiwar na Kwastam suka kama ƙwayar Tramadol 1,584,000 a filin jirgin.

A gefe guda kuma, NDLEA ta kama wani ɗan shekara 50 da yunƙurin shigar da hodar ibilis mai nauyin 11.91kg zuwa Ghana ta kan iyakar Seme da ke Legas.

A cewar sanarwar, waɗanda suka yi safarar ƙwayoyin sun yi amfani da motar jigilar kaya ta cikin filin jirgi mai suna Skyway Aviation Handling Compnay (SAHCO).

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending