News
YANZU-YANZU: Atiku ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa karo na shida
Daga Maryam bashir musa
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 a dandalin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, inda ya bayyana matakin da ya dauka a matsayin mai cike da tarihi tare da bayyana fatan ‘yan Najeriya za su taka muhimmiyar rawa wajen ganin ya aamu nasara.
Wasu ‘yan takara kamar Aminu Tambuwal, Dele Momodu, Bukola Saraki, Anyim Pius Anyim, da sauran ’yan takarar da aka ayyana da kuma wadanda ba a bayyana ba za su tunkari Mista Abubakar.
Masu sharhi kan harkokin siyasa suna tsammanin tarihin Mista Abubakar a matsayin dan siyasa mai dunkulewa amma mai cin hanci da rashawa, shari’ar cin hanci da rashawa da ya yi a Amurka ta hana shi shiga can.
Advertisements
