Tsohon shugaban Rasha Dmitry Medvedev, wanda a yanzu shi ne mataimakin shugaban kwamitin tsaro na kasar, ya ce “abin dariya” ne a dauka cewa matakan ladabtarwar da kasashen Yammacin Turai suka dauka kan kamfanoni da ‘yan kasuwar Rasha za su yi tasiri kan gwamnatin kasar.
Kasashen Yamma sun saka jerin takunkumai kan Rasha, wasunsu an saka wa manyan attajiran kasar ne wadanda a tunaninsu akwai wata alaka ta kut-da-kut tsakaninsu da Shugaba Vladimir Putin.
Ya ce “Bari mu tambayi kanmu: Shin akwai wani karfin fada a ji da wadannan ‘yan kasuwar ke da shi kan jagororin gwamnatinmu?”
“A bayyane, amsar ita ce: babu.”
Sai dai masu nazari na cewa matsawa ‘yan kasuwar na iya yin tasiri.
Stanislav markus, wanda ya dade yana nazarin attajiran na Rasha,ya shaida wa mujallar Amurka Vox cewa matakan ladabtarwan na damunsu sosai su kuma babu makawa gwamnatin Rasha za ta ji a jikinta.”
