Connect with us

News

An kashe wani mai zanga-zangar nuna kiyayya ga juyin mulki a Khartoum

Published

on

Daga aminu usman jibrin

 

 

Jami’an tsaron Sudan sun kashe wani mai zanga-zangar nuna kiyayya ga juyin mulki a ranar Alhamis a Khartoum.

Mutumin mai shekara 28 da haihuwa na cikin mutane 90 da aka kashe tun bayan da zanga-zanga ta barke domin nuna adawa da juyin mulkin da sojojin kasar suka yi wa gwamantin fara hula ta Abdalla Hamdok a watan Oktobar bara.

Sai dai duk da kashe-kashen, masu zanga-zangar ba su karaya ba.

Advertisement

A ranar Alhamis, dubban masu zamga-zanga sun yi maci zuwa fadar shugaban kasa a Khartoum, inda jami’an tsaro suka tarbe su da harsasai da hayaki mai sa hawaye.

Masu zanga-zangar na son sojojin su sauka, kuma su mika mulki ga gwamnatin farar hula.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending