Connect with us

Opinion

Harin bom na Abuja-Kaduna rail line shi ne ƙurunƙus!

Published

on

 

Babu rashin imanin da mai rai bai gani ba a kasar nan. Amma wannan harin ya ishe ka ka fahimci cewa mutanen da ke wannan abubuwa suna son su nuna mana ne ƙarara cewa idan za su samu dama to za su kashe duk wani mai rai a cikin kasar nan.

Advertisement

A taƙaice dai abinda na fahimta, masu aikata miyagun ayyuka nan, kisan mutane ne sana’arsu, shi ne jin daɗinsu fiye da komai. Kamar yadda na taɓa faɗa (kuma mutane da dama wadanda suka fi mu hangen nesa ma suka tabbatar) lalama ba ita ce mafita ba a cikin tinkarar su.

Ya rage na masu alhakin kawo mana karshen matsalolin nan. Ko dai su murƙushe su, ko kuma mutanen nan su ƙarasa durƙusar da kasar nan, duk su kakkashe mu.

Advertisement

Ba za mu gaji da addua ba. Allah Ya kawo mana karshen wannan tashin hankali. Ba za mu gaji da kira ba ga gwamanti cewa ko me ake yi don magance matsalar nan, to ba ya aiki. A canza tunani, a sake salo.

Allah Ya sa mu dace.

Advertisement

Daga salihu sule khalid

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending