Connect with us

Sports

Super Eagles: Augustine Eguavoen ya sauka daga muƙaminsa na kocin Najeriya

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Augustine Eguavoen ya sauka daga muƙaminsa sakamakon kasa kai tawagar Super Eagles gasar Kofin Duniya ta Qatar 2022.

Wata sanarwa da Nigeria Football Federation (NFF) ta wallafa a shafinta ta ce ta soke kwantaragin shekara biyu da rabi da ta bai wa kocin da tawagarsa nan take wanda tsohon ɗan wasan ƙasar ne.

“Za a sanar da sabuwar tawagar masu horarwa bayan duba cikin tsanaki don ɗora Super Eagles kan tafarki da zimmar fuskantar ƙalubalan da ke gabanta,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ambato Sakataren NFF Mohammed Sanusi na cewa “mun gode wa kociyoyin bisa aikin da suka yi wa ƙasa sannan muna yi musu fatan alheri a ayyukansu na gaba”.

Ana sa ran Eguavoen mai shekara 56 da ya horar da tawagar har sau biyu zai koma tsohon muƙaminsa na daraktan wasanni.

A ranar Talata ne Super Eagles ta kasa samun gurbin zuwa Qatar bayan tawagar Black Stars ta Ghana ta doke ta a Abuja babban birnin Najeriya.

Advertisement

An tashi wasa 1-1 a filin wasa na M.K.O Abiola bayan tashi 0-0 a wasan farko da giwayen na Yammacin Afirka suka fafata a birnin Kumasi na Ghana.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending