News
2023: Tinubu ya soki lamirin gwamnatin Buhari da sauran tsofaffin shugabannin Najeriya kan rashin cika alƙawari.
Daga Khadija abdullahi muhmd
Jigon APC kuma mai neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu, ya dangwali hancin Shugaba Muhammadu Buhari da sauran tsoffin shugabannin Najeriya a fakaice, inda ya ce zai cika alƙawurran da shugabannin Najeriya suka kasa cikawa, idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa.
Da ya ke magana a Legas, yayin da ya ke wa ɗaruruwan matasa jawabi waɗanda suka hallara domin nuna masa goyon baya, Tinubu ya ce, “Mu da ba matasa ba idan ku na cikin halin ɓacin rai, mu na ji a jikin mu. Ban ga laifin ku ba, alƙawurran da aka yi masu a baya aka kasa cikawa suka sa ku ka kasa cimma matsayin da ku ka so cimmawa tun ku na a ƙananan makarantu. Ba za mu dawwama mu na ta nuna ɓacin ran abin da aka kasa yi mana a can baya ba.”
A cikin wani bidiyon da aka nuno Tinubu na jawabi, wanda PREMIUM TIMES ta mallaka, Tinubu bai tantance ba tsakanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma gwamnatocin da suka gabata kafin Buhari ba.
Tinubu dai da Buhari duk a jam’iyya ɗaya su ke, kuma ya fito iya ƙarfin sa ya na so APC ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a 2023.
Baki Shi Ke Yanke Wuya: Maganar Da Tinubu Ya Kwalɓa Wa Buhari:
Tinubu ya ce alƙawurran da shugabannin baya suka yi duk ba su cika su ba, ballantana Najeriya ta bunƙasa.
Daga nan ya roƙi matasan su manta da wahalhalun da shugabannin suka jefa su a ciki.
Shugaba Buhari ya yi alƙawurra uku tun kafin ya hau mulki. Alƙawarin samar da tsaro, hana cin hanci da rashawa da kuma inganta tattalin arziki.
Yayin da ake fama da Boko Haram tun kafin hawan Buhari, bayan ya hau mulki kuma kashe-kashe da hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane ya ƙara muni sosai a ƙasar nan, musamman a Arewa. A Arewa ɗin ma a shiyyar Arewa maso Gabas, inda Buhari ya fito.
Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara taɓarɓarewar da tsadar rayuwa ta nunnunka, farashin kayan abinci sun yi tashin da talaka bai taɓa mafarkin za su yi ba, haka farashin fetur ya nunka zamanin Buhari, wanda ya yi alƙawarin idan ya hau zai rage masa farashi.
Yaƙi da cin hanci da rashawa kuma ya fuskanci matsaloli, inda ta kai kwanan nan har Buhari ya yi wa gwamnoni biyu da aka ɗaure afuwa, bayan kotu ta yanke masu hukuncin ɗaurin kama su da laifin satar biliyoyin kuɗaɗen talakawan jihar su.
“Ba zai yiwu mu ci gaba da haƙuri, juriya ko karɓar uzirin gazawar NEPA ta samar da wadatacciyar wutar lantarki ba. Babu ƙasar da za ta matsawa daga inda ta ke, matsawar babu lantarki a cikin ta. Ka samar mana wuta, idan muka kasa ci gaba sannan sai ka zage mu.
“Amma ka kasa samar mana wutar lantarki da za mu yi aikin bunƙasa ƙasa, kuma ka dawo ka ce mana raggwaye, ‘yan cima-zaune?” Haka dai Tinubu ya furta, furucin da kowa zai ce da Buhari ya ke, tunda shi ne a shekarun baya ya kira matasan Najeriya raggwaye.
Bayan Tinubu ya ce masu shi ne ya fi cancantar a zaɓa ya zama shugaban ƙasa a 2023, ya hori matasan da kowa ya je ya mallaki rajistar zaɓe.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
