News
Zaɓen 2023 a Najeriya: Ƴaƴan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya na ficewa saboda zargin ɗauki-ɗora.
Daga maryam bashir musa
Yayin da ake sa ran jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya za ta gudanar da taron majalisar zartarwarta, wanda shugabannin jam`iyyar suka ce zai mai da hankali wajen tattaunawa a kan shirin jam`iyyar na gudanar da zaben fitar da gwani domin tunkarar babban zaben 2023, wasu ‘yan jam’iyyar kokarin ficewa zuwa wasu jam`iyyu suke sakamakon zargin cewa ana musu dauki dora.
Barrister Soloman Dalong, tsohon ministan wasanni , kuma dan ga-ni-kashe-nin jam`iyyar APC, na daga cikin wadanda ke wannan zargi in da har ya shaida wa BBC cewa shi da APC fa haihata-haihata, har ma ya samu masauki a jam`iyyar SDP.
Tsohon ministan wasannin ya ce “Abin da yasa suka kafa jam’iyyar APC shine kama karyar da ake a jam’iiyarsu ta da, da kuma nada mutane a kan mukamai da babakere, shi ya sa muka fice daga waccan jam’iyyar muka kafa APC, to kuma sai gashi a kwana a tashi a ita jam’iyyar APC ma mun fara fuskantar waccan matsala.”
Ya ce,” Ba bu wanda zai ce maka komai sai kawai wadansu suje su zauna a daki su nada shugabannin jam’iyya, shi yasa naga bai kamata na ci gaba da zama ba a jam’iyyar APC ba.”
Bayan tsohon ministan wasannin akwai wasu sanatoci da wasu jiga-jigan jam`iyyar dai suka sauya sheka ko kuma suna kan hanyar yin hijira daga jam`iyyar APC irin su tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari da wasu.
Wannan lamari dai ya sa wasu `ya`yan jam`iyyar sun fara kira ga kwamitin zartarwar da ya dauki matakin gyara, idan ba haka to wankin hula ka iya kai jam`iyyar dare.
Alhaji Abdurrahman Buba Kwacham, jigon APC ne a jihar Adamawa, ya shaida wa BBC cewa, dole ayi hattara wajen barin shugabannin jam’iyya su zabi ‘yan takara wadanda suka dace da al’umma kuma suke so.
Ya ce,” Maganar dauki dora, to talakawan Najeriya ba zasu amince da ita ba a yanzu ba, sannan yana da kyau shugabanni su fahimci cewa babu Buhari a zaben 2023, yanzu kowa da jam’iyya ne da sunansa da darajarsa da kuma abin da ya aikatawa al’umma.”
Alhaji Abdurrahman Buba Kwacham, ya ce,” Don haka yanzu mutane ba jam’iyya suke nema su zaba ba, a’a suna nema su zabi mutane ne.”
Masana siyasa dai sun sha hasashen cewa za a kawo gabar da jam`iyyar APC za ta kure hakurin wasu `ya`yanta.
Shugabannin jam`iyyar APC dai kan bayyana cewa duk wata jam`iyyar da ta bunkasa ba a raba ta da rikici, ballantana irin ta jam`iyya mai mulkin kasa.
Sun kuma ce suna da yakinin za su iya shawo kan kowanne irin rikicin cikin gida.
